Amurka ta soki manufofin Najeriya kan ta'addanci

nigeria
Image caption Umar Farouk Abdulmutallab

Wani rahoto da gwamnatin Amurka ta fitar yayi suka ga manufofin Najeriya kan yaki da taaddanci.

A rahotonta na shekara shekara, ma'aikatar kula da harkokin wajen Amurkar ta ce dakarun yaki da ta'addanci na Najeriya, ba sa wani aikin a zo a gani, kuma majalisar dokokin kasar na daukar tsawon lokaci kafin ta amince da dokoki masu muhimmanci.

Haka kuma, rahoton ya nuna cewa, doka mafi tsanani ga yan ta'adda da masu sace mutane ita ce shekaru biyar a gidan yari.

Rahoton ya kuma soki Najeriyar, saboda rashin baiwa dakarun Amurka damar shiga kasar kai tsaye.

Rahoton yayi misali da yunkurin tarwatsa jirgin Amurka da wani dan Najeriya Umar Farouk Abdulmutallab mai alaka da Al'Qaeda, yayi.