Hukumar ICPC ta fara bincikar majalisar dokokin Najeriya

Nigeria
Image caption Tsohon shugban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya wato ICPC, ta ce za ta fara gudanar da bincike akan yan majalisar kasar bisa zargin cin hanci da rashawa da tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo ya yi musu.

Hukumar ta ce za ta gurfanar da duk dan majalisar da ta samu da laifi a gaban kuliya, da zummar yin hannun-ka-mai-sanda ga wasu jami'an gwamnati.

Sai dai yan majalisar sun ce suna maraba da wannan bincike.

A makon da ya gabata ne dai ,tsohon shugaban kasar ya zargi 'yan majalisar da cin hanci da rashawa, inda ya ce suna cusa wasu ayyuka a cikin na wasu ma'aikatu da sunan ayyukan raya mazabu, da nufin yin kashe-mu-raba da yan kwangila.