Ana zaman tankiya a PDP a jihar Kebbi

Rahotannai daga Kebbi na cewar zaman tankiyar siyasa ya kara kamari atsakanin bangarorin jam'iyyar PDP mai mulkin jahar masu adawa da juna bayan wasu hare- hare da magoya bayansu suka kaiwa juna a jiya inda aka lalata motoci fiye da arbain tare da raunata wasu mutane.

Lamarin dai ya faru ne a garuruwa Zuru da Ribah dake kudancin jahar sa'adda bangarorin biyu ke halartar wasu bukukuwa daban -daban ajiya.

Rahotannin suka ce magoya bayan tsohon Gwamnan jahar Senator Muhammadu Adamu Aliero sun kaiwa jerin motocin gwamnan jahar Alhaji Saidu Usman Dakingari hari a garin Ribah a zaman ramuwar gayya ga harin da suka ce magoya bayan bangaren gwamnan sun kai musu a garin zuru.