Ana jibga ruwa a Pakistan bayan ambaliya

Ruwan irin na malka na cigaba da zuba a arewacin Pakistan, inda tuni ambaliyar ruwa ta raba mutane da matsugunni, babu kuma abinci balle ruwan sha.

Hanyoyin da a da aka bude, an sake rufe su, kana jiragen saman helikwafta da ke aikin rabon agaji yanzu an dakatar da aikinsu.

Ambaliyar ruwan sai nufar kudancin kasar take yi, inda ta tilasta kwashe dubun-dubatar jama'a da lalata gonaki a lardin Sindh.

A ziyarar da ya kai lardin na Sindh, Firaminista, Yusuf Raza Gilani, ya yi kira ga jama'ar kasar da su nuna karfin hali.

Ya ce, "A irin wannan mawuyacin hali, kasar tana bukatar karfin zuciya. Lalle mu yi aiki tare don taimakon 'yan'uwa maza, da mata da kananan yara a wannan lokaci na tsanani."