An kammala zaben shugaban kasa a Rwanda

Rwanda
Image caption Wasu daga cikin mutane da suka rasu a kasar Rwanda a shekarar 1994

An kammala kada kuri'a a zaben shugaban kasa karo na biyu da aka gudanar a kasar Rwanda tun bayan yakin basasar shekerar 1994.

Ana sa ran shugaban kasar mai ci Paul Kagame, shi ne zai lashe zaben da gagarumin rinjaye, biyo bayan mutane ukkun dake takara da shi, dukkaninsu sun goyi bayansa a zaben da ya gabata.

Wakilin BBC a birnin Kigali Will Rose, ya ce yawancin masu sanya ido na ganin cewa, mutane ukkun dake takara da shugaba Kagame, ba komi bane illa don baiwa siyasar kimar jam'iyyu, bayan da aka haramtawa duk masu adawa da shi ta hakika takara.

Dubban jama'a ne suka ringa halartar taron yakin neman zaben shugaban, a yayinda masu adawa da shi ke samun daruruwa.

Masu goyon bayan shugaba kagame, suna yaba masa abisa kawo karshen yakin basasar da kasar ta yi fama da shi.