Wen Jiabao yana ziyara lardin Gansu saboda mirginowar kasa

A yanayin da ake ciki na matsanancin ruwan sama a yankin Asia a cikin shekaru da dama, Firaministan kasar Sin, Wen Jiabao, ya nufi lardin Gansu da ke arewa maso yammacin kasar, inda mirginowar kasa da tabo ta afkawa al'ummar Tibet, abin da ya jawo asarar rayuka da dama.

Mutane fiye da dari da ashirin ne suka rasa rayukansu.

Wakilin BBC ya ce, "Hotunan talabijin sun nuna yadda tabo da duwatsu suka mirgino daga kan tsauni bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya. Suka kuma rufe duk wasu gine-ginen da suka tari gabansu."