Amurka zata rage adadin kudin da take kashewa harkar tsaro

Image caption Sakatare tsaron Amurka Robert Gates

Amurka za ta zabtare adadin rundunar manyan sojojinta guda goma sannan ta rage kudaden da take kashewa akan sauran sassan ma'aikatar tsaron kasar.

Ta ce tana son ta samar da rarar kudade domin gudanar da yaki a fagen daga .

Sakataren tsaron kasar Robert Gates, ya bayyana cewa za'a dakatar da dakarun hadin gwiwa wato Joint Forces Command, sannan shelkwatar tsaron kasar wato Pentagon za ta rage bada kwangila da kashi goma cikin dari , sannan za'a rage adadin janar-janar na soji.