Koriya ta Kudu ta zargi Koriya ta Arewa da harba Igwa tekun Yellow Sea

Koriya ta kudu ta ce Koriya ta arewa ta harba makaman igwa zuwa tekun nan da ake kira Yellow Sea da turanci, watau tekun da Koriya ta Kudun ba ta dade da kammala wani gagarumin atisaye na jiragen yakin ruwa ba.

Al'amarin dai ya biyo bayan bukatar da Koriyata kudun ta gabatar ga ta arewa ne cewar ta maido da wani kwale-kwalen kamun kifi tare da matukansa bakwai 'yan Koriya ta kudu da yan China, wadanda ta kame a karshen makon nan.

Zaman zullumi ya kara muni ne tun a watan Mayu, a lokacin da aka yi zargin Koriya ta arewa ta nutsar da wani jirgin ruwan yaki na Koriya ta kudun, inda mtuane arba'iin da shida suka rasa rayukansu.