Majalisun dokokin Najeriya za su yi zaman gaggawa

Image caption Farfesa Attahiru Jega shugaban hukumar INEC

A yau majalisar dattawan Najeriya za ta yi wani zaman gaggawa, domin duba bukatar da hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta shigar ga bangaren zartarwar kasar.

Hukumar INEC dai ta nemi a bata naira biliyan saba'in da hudu, domin gudunar da wasu ayyuka, ciki har da sabunta rajistar masu zabe.

Majalisar dai ta katse hutunta ne domin gudanar da wannan aiki.

Sai dai a gobe ne wa'adin da hukumar zaben kasar ta bayar na a bata kudaden ke cika.