Mia Farrow ta bada shaida a kan Charles Taylor

Mia Farrow lokacin da take bada shaida
Image caption Mia Farrow itace ta raka Naomi Campbell zuwa wajen liyafar

Jarumar irin Finan-Finan da ke fitowa daga Amurka, Mia Farrow, ta bayar da shaidar da ta sabawa wadda Mai tallar kayan kawar nan, Naomi Campbell ta bayar a shari'ar da ake yiwa tsohon Shugaban Liberia, Charles Taylor a kan zargin aikata laifukan yaki.

A yayin da ta ke bayar da shaida a gaban kotun a birnin Hague, Mia Farrow, ta ce Naomi ta shaida mata cewar Charles Taylor ya aika mata da wani katon curin lu'u'lu'u bayan da suka kammala wani cin abincin dare a Afrika ta kudu a shekarar 1997.

A yanzu haka dai an samu baki biyu dangane da abinda ya wakana a gidan baki na gwamnatin a Afrika ta kudu da ke Pretoria a cikin watan Satumban 1997.

Abinda babu wata tantama akansa shi ne wasu maza biyu da suka kwankwasa kofar Naomi Campbell da tsakar dare sun danka mata duwatsun diamond da ba'a riga an sarrafa ba.

Maza sun kwankwasa mata kofa

Mia Farrow ta shaidawa kotu cewa washegarin faruwar hakan Ms Campbell ta ce mana Charles Taylor ya bata wani katon Diamond.

"Ta shaida mana cewa a cikin dare wasu maza sun kwankwasa mata kofa kuma Charles Taylor ne ya aikosu. sun kuma bata wani katon diamond."

Sai dai amakon jiya Naomi Campbell ta ce 'yan duwatsu ne aka bata kuma bata san wanda ya bata ba.

Tace a wajen kalaci na bada labarin abinda ya faru kuma ina jin ko ms white ko ms. Farrow ce ta ce ba mamaki Charles Taylor ne kuma duk yadda aka yi diamond ne.

Abinda ya sa wannan batun ke da muhimmanci shi ne, masu shigarda kara suna neman alakanta mista Taylor da diamond din ne domin kafa hujjar cewa ya tallafawa 'yan tawayen Sierra Leone a lokacin yakin basasar shekarun 1990.

Bayan shaidar ta Mia Farrow, yanzu kotun za ta saurari shaidar tsohuwar ajen din Naomi Campbell, wato Carol White.