Hukumar lekan asiri ta Isra'ila ta yi kaurin suna

Tambarin Mossad
Image caption Tambarin Hukumar leken asiri ta Mossad

A farkon shekarar nan ne dai aka kashe wani babban mamban kungiyar Hamas a Dubai. Ana zargin Mossad wato wata hukumar leken asirin Israela da alhakin kisan, duk kuwa da cewa gwamnatin Israelan tace babu shaidar hakan.

Hukumar Mossad din dai tayi kaurin suna, dangane da cewa ana matukar tsoran ta, sai dai kuma shin menene gaskiyar wannan, kuma ina kungiyar ta sa gaba?.

Rafi Eitan, ne ya jagoranci tawagar da ta kama Adolph Eichmann a Argentina. , wanda ya ke cikin wadanda suka kirkiro sansanin 'yan Nazi, wanda ke fuskantar shari'a a Isra'ila tun wadansu shekaru masu yawa da suka gabata.

"Mun hango shi yana sauka daga wata motar bus, yana nufar wurin da muka yi kwantan bauna domin kama shi. Zvi Malkin shine ya fara hambare shi, sannan mu uku muka dauke shi muka saka shi a cikin mota. Kansa yana kan cinya ta". In ji Rafi Etan

Hukumar leken asirin Israela wato Mossad, dai tayi kaurin suna ta wannan fuskar, wato yin aiyukan gaba gadi.

Amma a 'yan shekarun nan, ana yawan alakanta ta da kashe kashe, maimakon satar jama'a.

Zargin kashe jama'a

A kwanakin nan ne dai aka kashe wani babban Jami'in Hamas mai suna Mahmod al-Mabouh, a Dubai.

Mabhouh dai ya sauka ne a wani otal dake kusa da tashar filin jirgin saman garin. Duk iya tsawon lokacin kasancewarsa a can, ana lura da shi.

Ya shiga cikin naurar da ke hawa da sauka da mutane dake otal din, ya fita a hawa na biyu. Mutane biyu sanye da irin kayan wasan Tennis na biye dashi a baya zuwa dakin da ya sauka.

Matar Mabhouh dai ta tuntubi otal din ne bayan da ta kasa samun mijinta a waya. Daga nan ne aka bincika dakinsa, sai aka tsinci gawarsa.

Image caption Jami'in Mossad ya cafke wani

Doctor Saeed Hamiri wani dan sanda a Dubai ya ce ; "An binciki gawar ne a gaban wadanda ke bincikar miyagun laifuka. Sun bayyana cewa dakin dai a kulle yake a lokacin, sai dai akwai alamomi da dama dangane da kisan. Akwai jini a jikin Pillow dake kan gadon dakin, ya samu raunuka a hancinsa, da fuskarsa dama wuyansa, sannan kuma akwai alamun soka masa allura a cinyarsa. Sannan kuma alamar lalata saman gadon ma na nuni da kokarin kubcewa".

Kyamarorin CCTV dai na nuni da cewa an yi ta bin Mabouh ne tun daga filin jirgin sama har ya zuwa otal din.

Da taimakon hotunan da kyamarar ta dauka, da kuma fasfo, an gano wadansu daga cikin masu sanye da irin kayan 'yan wasan Tennis din. 'Yan Sandan Dubai dai sun ce shaidun da suka samo na nuni da hukumar Mossad ce.

Tuni dai iyalan Mabouh suka dauki wani lauya dan Birtaniya mai suna Tayab Ali domin bin diddigi.

"Suna da sauran zabi. Zasu iya tambayar jami'an Dubai in sun san inda Mahmoud al Mabhouh yake, zasu iya ce musu su tsare musu shi. Ko da kuwa babu yarjejeniyar mika mai laifi domin ya fuskanci sharia a tsakanin kasashen biyu, zasu iya nema. Ba wai ina cewa Isra'ila ta dauke mutum ba bisa doka ba, amma ai abinda ya faru akan Eichmann kenan".

Isra'ila ta musanta zargi

Isra'ila dai tayi ta nanata cewa babu shaida akan kisan. Sai dai kuma Birtaniya ta sallami jami'in hukumar Mossad din dake London, a saboda shaidar da ta samu akan hukumar na yin amfani da Fasfon Birtaniya.

Mishka Ben David wani tsohon Jami'in Mossad ya ce; "Ban sani ba ko ya kamata ace na rubuta ta wata fuska. Wannan aiki ne na bajinta, wanda daya daga cikin abubuwan da ake tunani bai yi daidai ba, ba wai don naurar CCTV ta bayyana haka ba, sai dai zai iya kasancewa karar kwana ce".

Rahotannin kwana kwanan nan dai na bayyana cewa shugaban hukumar Mossad din Meir Dagan, zai sauka daga mukaminsa a saboda wadansu dalilai da ba'a bayyana ba.

Sai dai duk da haka, an samu rauni a alakar diplomasiyya daga bangaren Dubai, sannan kuma babu wata alama dake bayyana cewa kungiyar Mossad din za ta sauya yanda take abubuwanta.