Jami'an Nijar sun tattauna tare da takwarorinsu na Najeriya

A Jamhuriyar Niger an kammala wani zaman hukumar hadin gwiwa tsakanin Niger da tarayyar Najeriya, karo na talatin da biyar a birnin Yamai.

Wasu daga cikin muhimman kudurorin da taron ya dauka sun hada da sanya hannu a kan wata yarjejeniyar gudanar da sintiri na jami'an tsaron kasashen guda biyu a kan iyakokin Niger din da Najeriya.

A bangare guda kuma, Gwamnatin Nijeriya ta bada sanarwar baiwa kasar ta Niger tallafin dala miliyan Hudu da kuma kayan abinci kimanin tan dubu goma na gero da shinkafa da kuma Masara domin taimakama Kasar yaki da Yunwa.