Kwamitin Amintattu na Jam'iyyar PDP zai yi taro

Nigeria
Image caption Postar shugaban kasar Najeriyar Goodluck Jonathan

A yau ne dai ake sa ran kwamitin Amintattu na jamiyyar PDP zai yi wani taro a Abuja.

Kuma ana sa ran daya daga cikin manyan batutuwan da za'a tattauna akai shi ne tsarin mulkin karba-karba.

Tsarin mulkin na karba-karba a yanzu haka, shine ya mamaye fagen siyasar Nigeriar a yayinda wasu na son a cigaba da amfani da tsarin , wasu kuwa na neman shugabannin jam'iyyar su yi fatali da shi.