'Yan sanda a Nijeriya na taro kan zaben 2011

A Nijeriya ana gudanar da wani taro don wayar da kan manyan jami`an `yan sanda da na ma`aikatar `yan sanda ta kasar kan irin rawar da za su iya takawa a wajen babban zabe na kasar dake tafe.

Hukumomi a Nijeriyar dai sun ce taron wani bangare ne na shirye-shiryen da ma`aikatar `yan sandan ke yi don tunkarar kalubalen babban zaben kasar na badi.

Ana dai zargin `Yan sanda a Nijeriyar da kasancewa da hannu a magudin zabukan da aka yi a baya .