An kashe mutane biyu a Gusau kan siyasa

Mutune biyu ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu kuma da dama suka raunata a wani fada tsakanin magoya bayan gwamnatin jam'iyyar PDP a jihar, da na Jam'iyyar adawa ta ANPP a Gusau babban birninta.

Haka nan kuma an lalata wasu motoci a sakamakon rikicin da ya faru lokacin 'yan jam'iyyar ta ANPP ke shirin tafiya wajen wani taron kaddamar da dan takarar Gwamnan jihar a yau.

Rahotanni sun ce wasu 'yan jam'iyar PDP mai mulki ne suka nemi hana su wucewa domin zuwa wurin taron, lamarin da ya haddasa artabu tsakanin bangarorin biyu.