Ambaliyar ruwa a Yammacin Afrika

Amfanin gona
Image caption Wannan na nufinmai yiwuwa a samu amfanin gona mai yawa a nahiyar Afrika

Sabanin yadda masana suka hanga, daminar bana ta zo da karfi sosai a yankin Yammacin Afirka, inda a kasashe da dama ake ta samun ruwa kamar da bakin kwarya.

Wakilin BBC Richard Hamilton ya ce, dubban mutane sun rasa gidajensu, kuma har yankunan da sukai fama da fari sun fuskanci matsalar ta ambaliyar ruwa.

A tsakiyar kasar Guinea, ruwa da kankara wadda girmanta ya kai girman kwai sun lalata amfanin gona, yayinda a Arewacin kasar Chadi daura da hamadar Sahara, aka tafka ruwan da ba a taba ganin irinsa ba a shekaru hamsin.

Ruwan ya tilastawa mazauna garin Faya-Largeau mai dausayi da ke Arewacin kasar ta Chadi tserewa daga gidajensu da kuma kwana a waje a tsakankanin tarin yashi.

Asarar rayuka

Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta ba da rahoton cewa fiye da mutane 800 ne suka rasa muhallinsu a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka.

Haka nan kuma kungiyar ta samar da agajin hemomi da kayan girki ga wasu al'ummun kasar Ivory Coast, inda wasu mutane suka rasa rayukansu sanadiyyar zamewar tabo.

A Nijar ma fiye da gidaje dubu daya ne suka rushe yayin da matsalar ta shafi fiye da mutane dubu biyar.

A Nijar din, Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da dabbobi dubu talatin sun mutu kuma ana iya ganin gawarwakinsu suna linkaya kusa da idaniyar ruwa.

A Najeriya kuwa ambaliyar ruwa jifa-jif a ta haifarwa manoma kusan dubu dari asarar amfanin gonarsu; yayinda a Ghana fiye da mutane arba'in suka rasa rayukansu.

Rashin magudanan ruwa

A jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Najeriya, jama'a da dama sun fuskanci matsalar ambaliyar ruwa, wacce ke ci gaba da jefa su cikin wahala.

Image caption Amma ruwan kamar da bakin kwarya ya haifar da asara ga manoma da dama

Jama'ar dai sun dora alhakin lamarin kan rashin kyawawan magudanen ruwa a yankunan nasu.

Sakamakon cikar madatsun ruwa biyu a Burkina Faso, hukumar ba da agajin gaggawa ta Ghana ta yi gargadi ga al'ummun da ke jihohi uku na Arewacin kasar.

Gwamnatin Burkina Faso ta bayyana cewa akalla mutane goma sha hudu sun rasa rayukasnu yayinda wasu da dama ke kwana a makarantu sakamakon ambaliyar ruwan.

A ranar Litinin kuma akalla mutane 13 ne suka rasu lokacin da wani gida ya fada musu a ka a Freetown, babban birnin kasar Saliyo.