An gurfanar da Omar Khadr a gaban kotun soja

Omar Khadr
Image caption Omar Khadr

An gurfanar da Omar Khadr, wanda shi ne fursuna na farko a sansanin Guantanamo da ya gurfana a gaban wata kotun soja, karkashin mulkin shugaba Obama.

Shi dai shugaba Obama yayi alkawari ada cewar zai rufe sansanin a farkon wannan shekarar.

An kama Omar Khadr ne, wanda ke takardun zama dan Canada, a lokacin da yake da shekaru 15, bayan wani artabu a Afghanistan, shekaru 8 da suka wuce.

Mr Khadr dai ya ki amsa laifufukan da ake tuhumar shi da su.