An amince da afuwa ga sojojin Nijar

Majalisar tuntubar juna a jamhuriyar Nijar ta amince da yin afuwa ga sojojin da suka aiwatar da juyin mulki a kasar, a matsayin wani bangare na tanajin sabon kudin tsarin mulkin da take nazari a kai.

Haka nan kuma ta amince da shawarar da aka bayar ta haramta wa duk wanda ya haura shekaru saba'in tsayawa takarar shugaban kasa , da na majalisar dokoki.

Majalisar ta yi hakan ne a muhawarar da take ci gaba da yi a Yamai.