Gini ya kashe mutane 8 a Najeriya

Gini ya kashe mutane 8 a Najeriya
Image caption Jami'an agaji na kokarin ceto wadanda ginin ya rufta da su

Akalla mutane takwas ne suka mutu yayinda da dama suka samu raunuka bayan da wani gini mai hawa uku ya rufta a Abuja babban birnin Najeriya.

Ginin wanda ba'a kammala ginawa ba na dauke da mutane kusan 40 a unguwar Area 11 da ke kusa da tsakiyar birnin Abuja, ya rufta ne da asubahin ranar Laraba.

Ministan da ke kula da birnin na Abuja, Sanata Bala Muhammad, wanda ya ziyarci wurin ya shaidawa manema labarai cewa mutane takwas ne kawo yanzu suka rasa rayukansu.

Sanata Bala ya kara da cewa tuntuni mahukunta suka gargadi mazauna gidan da su fice domin gidan na cikin hadarin faduwa.

Amma suka yi kunnen uwar shegu da gargadin, abinda yasa ministan yace hukumar birnin za ta dauki matakai masu tsauri domin shawo kan irin wadannan matsaloli anan gaba.

Jami'an tsaro daban daban da kuma kungiyar agaji ta Red Cross, wadanda ke taimakawa wajen zakulo wadanda lamarin ya ritsa da su, na ci gaba da kaiwa jama'a dauki.

An dai sha samun ruftawar gine-gine a Najeriyar abaya, abinda masu lura da al'amura ke dangantawa da rashin bin ka'idojin gini da kuma rashin amfani da ingantattun kayayyaki yayin gina gidajen.