An yi garambawul a majalisar ministocin Najeriya

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya
Image caption Babu tabbas ko shugaba Jonathan zai tsaya takara a zabe mai zuwa ko kuma a'a

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yiwa majalisar ministocin kasar kwarya-kwaryar garambawul, inda ya nada mata biyu 'yan jam'iyyar adawa ta ANPP daga Arewacin kasar da kuma namiji guda dan jam'iyyar sa ta PDP daga bangaren kudancin kasar.

Wannan nade-naden na zuwa ne daidai lokacinda ake shirin gudunar da zaben shugaban kasar a watan Janairun badi.

A ranar Laraba ne dai shugaban ya rantsar da sabbin ministoci ukun, abin da ya kara adadin ministocin daga 39 zuwa 42.

Ministocin sun hada da tsohuwar minista a zamanin marigayi shugaba Umaru Yar'adua Hajiya salamatu Suleiman daga jihar Kebbi, wacce yanzu aka nada karamar ministar hulda da kasashen ketare.

Dayar kuma itace Mrs Yabawa Wabi daga jihar Borno wacce ta maye gurbin karamin minsta kudi Remi Babalola da aka mayarda shi ministan ayyuka na musamman.

Shi dai Remi Babalola shi ne ya haifar da cece-kucen da ya tada jijiyar wuya tsakanin kamfanin mai na Najeriya NNPC da kuma gwamnati a gefe guda, bayan da ya bayyana cewa kamfanin ya tsiyace.

Gwamnatin dai ta fito ta yi watsi da kalaman nasa, abinda kuma masu lura da al'amura ke ganin shi ne dalilin da ya sa aka sauya masa wurin aiki.

Wannan nade-naden dai sun zo ne a lokacin da ya rage watanni biyar a gudanar da zaben shugaba kasa a Najeriyar, zaben da yiwuwar tsayawar shugaba Jonathan a matsayin takara ke ci gaba da jawo kace-nace a kasar.

Sai dai kawo yanzu shugaban bai fito fili ya bayyana cewa zai tsaya ko ba zai tsaya takara a zaben mai zuwa ba.