Damuwa kan rejistar masu aikin Hajji a Nijer

Taswirar Jumhuriyar Nijer
Image caption Ranar 13 ga wannan watan ne aka shirya zaa kammala rejistar maniyata

A jamhuriyar Nijar masu kamfanonin hajji da Umara sun yi kira ga gwamnati da ta kara musu lokaci domin bai wa maniyata aikin hajjin bana damar yin rejista.

Yanzu haka dai dai gwamnatin Nijer din ta tsaida jibi juma'a 13 ga wannan watan a matsayin ranar da ya kamata dukan kamfanonin hajjin su mika ma ta sunayen alhazan da za su yi hajjin ta hannunsu.

Gwamnatin ta dauki wannan matakin ne domin kauce ma lattin da alhazan Nijar ke yi kowace shekara , wanda ke kawo cikas ga masu kamfanonin hajjin,da gwamnati,da ma hukumomin Saudiya wajen daukar matakan sauke alhazan na Nijar a kasa mai tsarki.