Kwamitin amintattu na PDP ya amince da tsarin Karba-Karba

Jam'iyyar PDP
Image caption Jam'iyyar PDP

Kwamitin Amintattu na jam`iyyar PDP mai mulki a Nigeria ya amince da ci gaba da tsarin karba-karba akan shugabanci tsakanin shiyyoyin kasar.

Kwamitin ya goyi bayan da a ci gaba da barin sashen da da ya halalta tsarin karba-karba ya a cikin kundin tsarin mulkin jam`iyyar.

Sai dai kwamitin ya bayyana cewa shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan yana iya tsayawa takara a babban zaben kasar na badi.

A jiya ne dai kwamitin ya cimma wannan matsaya a wani zama da aka kai talatainin dare a Abuja babban birnin kasar.

Ana sa ran taron kwamitin zartaswa na jam'iyyar da za'a yi a ranar Alhamis zai tattauna akan wannan magana da nufin fitar da matsaya.

Shugaba Goodluck Jonathan dai bai bayyana cewar zai tsaya takara ba ko kuma a'a a zaben shugaban kasar da ake sa ran yi a farkon shekara mai zuwa.