An sabunta: 12 ga Agusta, 2010 - An wallafa a 08:31 GMT

Nijar:Ambaliyar ruwa ta raba mutane da gidajensu

Ambaliyar ruwa ta raba mutane da dama da muhallansu

Ambaliyar ruwa ta raba mutane da dama da muhallansu

A Jamhuriyar Nijar, ambaliyar ruwan da ta aukawa wasu yankunan kasar sakamakon cika da batsewa da kogin kwara yayi, ta sa dubban iyalai sun rasa muhallansu da kuma kadarorinsu.

A yanzu haka wadannan al'ummomi na zaune ne a wasu matsugunai na wucin gadi kamar makarantu da hukumomi suka tanadar, yayin da a wasu jihohin kuwa tuni gwamnati da wasu kungiyoyin agaji suka fara kone gawarwakin dabbobin da suka mutu.

Wasu masana fannin kiwon lafiya sun fara bayyana fargabar barkewar cututuka a wadannan wurare, matukar hukumomi basu dauki kwararan matakai ba.

Dakta Iliyasu Idi Mainasara, babban sakataren hadaddiyar kungiyar kwararrun likitocin Nijar ya yi kira ga gwamnati ta dauki matakan kiwon lafiyar mutane kafin cututtuka su barke.

Ambaliyar ruwa a Nijar

 • Ambaliyar ruwa a Nijar
  A Nijar fiye da gidaje dubu daya ne suka rushe sanadiyar ambaliyar ruwa. Idy Bara'u ne ya dauko mana hotunan.
 • Ambaliyar ruwa a Nijar
  Matsalar ta shafi fiye da mutane dubu biyar.
 • Ambaliyar ruwa a Nijar
  Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da dabbobi dubu talatin sun mutu a ambaliyar ruwan.
 • Ambaliyar ruwa a Nijar
  Kungiyar UMMA WEALTH TRUST UK, ta baiwa kasar Nijar agajin kayyayakin abinci harma da Tuffafi domin agazawa mutanen da yunwa da ambaliyar ruwa suka shafa a kasar .

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.