Kiran bada agaji ga Pakistan

John Holmes a Pakistan
Image caption John Holmes a Pakistan

Majalisar Dinkin Duniya, ta nemi a bada agajin gaggawa na dala miliyan dari hudu da sittin, domin taimaka ma Pakistan, mai fama da matsalar ambaliyar ruwa, wajen magance matsalolin da take fuskanta na muhallai da kuma abinci.

Shugaban hukumar ayyukan jinkai ta MDD John Holmes ya yi kira ga al'ummar duniya da ta taimaka wajen cike gibin da aka samu a kokarin da Pakistan ke yi na taimaka ma al'umarta.

Ofishin kula da ayyukan jinkai na MDD ya ce wannan ambaliyar ruwa ita ce mafi muni a kasar a shekaru masu yawa.

Mutane miliyan goma sha hudu ne lamarin ya shafa, yayinda mutane dubu daya da dari biyu suka mutu.