Kalubalen dake gaban hukumar zaben Najeriya

Kalubalen dake gaban hukumar zaben Najeriya
Image caption Farfesa Jega yayi alkawarin tabbatar da adalci a zeben mai zuwa

Adaidai lokacin da ya rage kasa da watanni shida kafin a gudanar da babban zaben kasa ba ki daya a Najeriya. A yanzu hankali na kara karkata kan hukumar zabe mai zaman kanta ta Inec.

Tun bayan da aka nada Farfesa Attahiru Jega a matsayin sabon shugaban hukumar watanni biyu da suka wuce, hukumar ta sha alwashin gudanar da zabe mai inganci a kasar.

A baya dai an sha zargin hukumar da kasa shirya zabuka masu adalci, musamman ma a lokacin zabukan shekara ta 2007, inda 'yan kallo na cikin gida da waje suka yi Allah wadai da rawar da hukumar zaben ta taka.

'Yan kasar da dama na fatan sabon shugabancin da aka samu a hukumar zai kawo sauyin da a cewar masu lura da al'amura aka dade ana jiran samunsa.

Tunkarar zabe kai tsaye

Tuni dai hukumar zaben karkashin jagorancin Attahiru Jega ta fara daukar matakan da a cewarta za su bata damar gudanarda da zabe main inganci a watan Janairu mai zuwa.

Matakan da hukumar da fara dauka sun hada da na amincewa da gudanar da sabuwar rijistar masu zabe, wacce kusan ita ce kashin bayan shirye-shiryen zaben.

Image caption Abaya an zargi hukumar zaben da gazawa wajen gudanar da adalci a zabukan da ta shirya

Haka kuma hukumar ta gabatar da kasafin kudaden da take bukata daga gwamnati domin gudanar da zaben baki dayansa. Tare da neman lallai a bata kudaden kafin 11 ga watan Agusta, idan har anason zaben ya gudana kamar yadda aka tsara.

Sai dai duk da cece kucen da ake tayi game da kasafin da hukumar ta gabatar a gaban Majalisun Dokokin Kasar, majalisun sun amince a baiwa hukumar naira biliyan 87 domin shiryawa zaben na badi.

Da farko dai an nuna shakku kan yadda hukumar ta ware wasu makudan kudade da tace na ko ta kwana ne, da kuma ribar da za a baiwa 'yan kwangila.

Kuma hakan ya sanya alamar tambaya kan yadda manyan daraktocin hukumar ke sarrafa akalar sabon shugaban nata, sai dai Farfesa Jega ya yi watsi da wannan zargi yana mai cewa kawo yanzu baiga wata alamar zagon kasa daga abokan aikin nasa ba.

Maida hankali

To ganin cewa a yanzu an amince da bukatar hukumar zaben na bata wadannan kudade da take bukata, ko menene ya kamata ta maida hankali a kai.

Image caption Najeriya ta sha suka daga kasashen duniya kan zabukan shekara ta 2007

Malam Faruq BB Faruq, malami ne a sashin siyasa na jami'ar Abuja, kuma ya ce akwai nauyi da yawa da ya kamata hukumar ta INEC ta sauke.

Yace hakaika lokacin da ya rage ba shi da yawa, kuma an basu kudaden da suke bukata, amma duk da haka gwamnati na da rawar da za ta taka ganin cewa itace take da mallakin jami'an tsaro da sauran ma'aikata.

"Ya kamata shugaban hukumar zabe ya fito fili ya tabbata cewa an yi aiki tukuru, ba tare bata lokaci ba, domin tabbatar da cewa an yi zabe mai inganci".

'Kudi ake nema kuma an bayar'

Malam BB Faruq ya kara da cewa dama dai hukumar kudi ta ke nema kuma an bata, don haka basu da wata mafaka idan ba su yi abinda ya dace ba.

"A gani na lokacin da ya rage ya isa hukumar ta gudanar da zabe mai inganci, tunda dai akwai komai da komai a kasa, ganin cewa shekaru kusan goma kenan da kafa hukumar," in ji BB Faruq

Baya ga jami'an hukumar zabe dai, sauran 'yan kasar ma na da rawar da za su taka wajen tabbatar da wannan lamari.

Daga cikin rawar da za su iya takawa ta hada bada hadin kai wajen fita domin yin rijista, sannan su kasa su tsare, su kuma raka a lokacin zabe.

Har ila yau jami'an tsaro ma na da rawar takawa ganin cewa a baya an zargesu da laifin hada baki da wasu 'yan siyasa wajen yin magudi.

Masu lura da al'amura dai na ganin muddum shugabannin hukumar zaben basu yi ta baza ba, to ba lallai bane a cimma burin da ake fata ba na samun ingantaccen zabe ba.