An tisa keyar dan leken asirin Isra'ila zuwa Jamus

An tisa keyar wani mutum da ake kyautata zaton dan leken asirin Isra'ila ne zuwa Jamus bisa zargin kasancewa da hannun a kisan wani kusa na kungiyar Hamas a Dubai.

Hukumomin Poland ne suka mika mutumen mai suna Uri Brodsky.

Masu shigar da kara a Jamus dai na zargin shi da laifin samun fasfo na Jamus ba bisa ka'ida ba, wanda kuma wadanda ake zargi da kashe Mahmoud al Mabhouh a watan Janairu, suka yi amfani da shi.

Ana zargin cewa 'yan kungiyar leken asirin Isra'ila na MOSSAD ne suka kashe shi, amma Isra'ila ta ce babu wata hujja dake tabbatar da hakan.

Isra'ila dai ta fuskanci matsin lamba daga kasashen Yammacin duniya da dama, bayan da aka gano cewa makasan sun yi amfani da fasfo na wadannan kasashe.