Majalisar Dinkin Duniya ta raba kayan agaji a Chadi

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce tana rarraba muhimman kayan agaji ga iyalai dubu biyu da rabi da mummunar ambaliyar ruwa ta ritsa da su a kasar Chadi.

Kayan agajin sun hada da barguna da kuma abubuwan shimfida na leda.

Tun tsakiyar watan Yuli ne dai, ambaliyar ruwan ta afka wa yankuna da dama na kasar ta Chadi, sakamakon saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya, wanda ba a taba yi ba a cikin shekaru 40 da suka wuce.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniyar ta ce ayyukan rarraba agajin na fuskantar cikas, saboda mummunan yanayin da ya biyo baya.

Jumhuriyar Nijer da Jumhuriyar Afrika ta Tsakiya, suma sun yi fama da matsalar ta ambaliyar ruwa.