Masana sun yi gargadi kan bangar siyasa

Masana sun yi gargadi kan bangar siyasa
Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, masana harkokin siyasar kasar sun yi gargadi kan yin amfanin da matasa wajen yin bangar siyasa.

Masanan sun zargi 'yan siyasar da yin amfani da matasan, inda suka ce suna yin hakan ne don cimma wani buri na su.

Dakta Hussaini Abdu , wani mai sharhi akan siyasa ya ce muddin 'yan siyasa basu daina amfani da matasa wajen yin bangar siyasar ba, kasar za ta fuskanci tashe-tashen hankula a zaben shekara ta 2011.

Jihohi da dama sun fuskanci tashe-tashen hankula sakamakon taho-mu-gama a tsakanin magoya bayan 'yan siyasa masu mabambantan ra'ayoyi.