Watan Ramalana: Kayan masarufi na tsada a Sakkwato

Matsalar hauhawar farashin kayan masarufi a lokacin azumin wata ramadana dai batu ne da musulmin arewacin Najeriya ke kokawa dashi a duk shekara.

Jahar Sakkwaton Najejriya na daya daga cikin inda ake samun wannan matsalar kuma a kodayaushe a kan dora laifin hauhawar farashin ne kan yan kasuwa masu neman kazamar riba.

A kan haka ne a wannan shekarar kungiyoyin yan kasuwa a jahar suka yi wani taro inda suka amince da daukar matakan hana hauhawar farashinkayan ciki har da kafa wani kwamitin da zai rika zagaya kasuwanni domin tabbatar da farashi bai hau ba.