Jami'an Lebanon sun kashe dan kungiyar Fatah Al-Islami

Dakarun Lebanon
Image caption Dakarun Lebanon

Jami'an tsaron Lebanon sun ce dakaru sun kashe wani muhimmin shugaban kungiyar 'yan gwagwarmayar Islama ta Fatah Al-Islam dake samun goyon bayan Al-Qa'ida.

Sun ce an harbe mutumin, Abdel Rahman Awad har lahira ne tare da wani dan gwagwarmayar a wani artabu da bindigogi a garin Chtaura a kwarin Bekaa.

Abdel Rahman Awad na daya daga cikin mutanen da aka fi nema ruwa a jallo a kasar ta Lebanon, kuma kamar yadda wasu majiyoyi suka ce ya zama Shugaban kungiyar Fatah al-Islam ne a shekara ta dubu 2007.

A farkon wannan shekarar, kungiyar ta kafsa fada na tsawon watanni uku tare da sojin Lebanon, wanda aka kashe mutane da yawa a cikinsa.