Matasa sun koka kan rashin aiki a Najeriya

Taswirar Najeriya
Image caption Matasa sun koka kan rashin aikin yi a Najeriya

A Najeriya, matasa sun koka kan rashin samun aikin yi musamman ga wadanda suka kammala karatun jam'ia.

Matasan sun shaidawa BBC cewa duk da tallafin da gwamnatoci ke ikirarin baiwa jama'a domin dogaro da kai,har yanzu basu samu tallafin ba.

Galibin matasan sun koka cewa, matsaloli daban-daban sun dabaibaye su,inda suka ce hakan zai iya ingiza wasunsu ga aikata miyagun laifuffuka.

Mista Onyedika Agbo, wani matashi ne, kuma ya ce, ''wajibi ne gwamnati ta san da zaman mu, sannan ta bullo da hanyoyin tattara bayanai akan mu; ta san matsalolinmu. Haka kuma ta dauki matakan samar mana da ayyukan yi''.