Obama ya goyi bayan gina masallaci a New York

Shugaban Amurka,Barack Obama
Image caption Shugaba Obama ya goyi bayan musulmi don gina masallaci a Newyork

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama, ya goyi bayan shirin al'ummar Musulmi na gina masallaci a kusa da wajen da aka kai harin ta'addancin ranar sha daya ga watan Satumban shekarar 2001.

A yayinda da yake magana a kan batun, Mista Obama ya ce kokarin Amurka na baiwa kowa 'yancin gudanar da addininsa abu ne da ba zai sauya ba.

Ya ce hakan kuwa ya hada da barin mutane su gina wuraren ibadarsu.

Ya kuma ce kuskure ne a rika kallon dukkan musulmai a matsayin 'yan ta'adda kamar 'yan kungiyar Al-Qa'ida.

Sai dai masu kamfe din ganin ba a gina masallacin ba na ci gaba da yin hakan, duk da yake yunkurin nasu bai yi wani tasiri ba.

'Yan adawa sun soki Shugaba Obama a kan batun, inda suka ce ba shi da da'a, kana bai ji tausayin wadanda aka kashe yayin harin ba.