Pakistan ta soki kasashen duniya

Ambaliyar Pakistan
Image caption Kimanin mutane miliyan takwas ne bala'in ya ritsa da su

Wasu manyan Jami'an kasar Pakistan sun soki kasashen duniya kan abin da suka kira jan kafa da kasashen ke yi wajen taimakawa wadanda bala'in ambaliyar ruwa ya aukawa.

Jakadan Pakistan a Majalisar Dinkin Duniya Zamir Akram, ya shaidawa BBC cewa kawo yanzu ba'a samu isasshen taimakon da ake bukata ba.

Kungiyoyin agaji sun yi gargadin barkewar cututtukan dake da alaka da rashin tsaftataccen ruwan sha.

Ya ce mutane da dama basu fahimci girman yadda lamarin yayi kamari ba, sanann yayi watsi da hasashen da wasu ke yi cewa, zargin da akaiwa kasar na alaka da kungiyar Taliban yasa kasashen duniya sun yi watsi da ita.

'basu fahimci illar bala'in ba'

Yace ina ganin jama'a a duniya bawai kawai gwamnatoci ba, harma da kungiyoyin farar hula, da masu zaman kansu, basu fahimci irin mummunar illar da wannan bala'in ya haifar ba.

Ya kara da cewa kimanin mutane miliyan hudu ne abin ya ritsa da su, adaidai lokacin da ake kara fuskantar yiwuwar wata ambaliyar a yankunan Punjab da Sind.

Kasar ta Pakistan dai ta fasa gudanar da bukin zagayowar ranar samun 'yan cin kai, sakamakon afkuwar wannan bala'in.

Amaimakon haka shugaba Ali Zardari, zai shafe ranar ne da iyalin wadanda abin ya ritsa da su.