Mutane miliyan ashirin ambaliyar ruwa ta shafa a Pakistan

A halin yanzu dai mutane miliyan ashirin ne mummunar ambaliyar ruwa ta shafa -- karin miliyan shida da tun farko aka tsammata.

Sababbin alkaluman da Firaministan, Yousuf Raza Gilani, ya bayar a cikin wani jawabi na tunawa da zagayowar ranar da kasar ta samu yancin kai, wadda kuma aka yanke shagulgulan ta matuka.

Ya ce har yanzu akwai mutanen da ambaliyar ruwan ta rutsa da su da ba kai gare su ba, to amma Gwamnati za ta yi dukan abinda za ta yi.

Ya ce, ina mai tabbatar wa kasar nan cewar mu, gwamnatin Dimukuradiyyar ku, za ta yi dukanin abinda ta iya ta hanyar tallafawa jama'a daga wannan bala'i.

Tun farko wani babban jami'in Pakistan ya soki abinda suke gani tafiyar hawainiyar kai daukin kasashen duniya ga bala'in.