Mutane goma sun mutu sakamakon hari a Pakistan

Mutane akalla goma ne aka bayar da arhoton an harbe har lahira a kudu maso yammacin Pakistan a wani hari a kan wata motar bas din fasinja.

Haka kuma an raunata wasu fasinjojin da yawa a lokacin da wani gungun mazaje dauke da makamai ya bude wuta a kan bas din, kudu maso gabacin Quetta babban birnin lardin Balochistan.

An ruwaito wani jami'i na cewar yan bindiga kusan 35 ne keda hannu a lamarin. Babu dai wata kungiyar da ta ce ita ce ta kai harin.

A jiya juma'a mutane da yawa , hade da akalla yansanda 3 ne aka harbe a wasu hare hare biyu daban daban a Quetta.