An sami baraka a jam'iyyar PNA al'umma a Nijer

A jamhuriyar nijar an samu baraka a cikin jam'iyar PNA Al'uma ta Alhaji Sanusi Tambari Jaku.

Wasu mambobin kwamitin gudanarwa na Jama'iyar su 22 ne suka fitar da sanarwa yau din nan a Yamai cewa sun koma jam'iyar PNDS Tarayya inda suke jin za su fi samun biyan bukata a harkokinsu na siyasa.

Daga cikin dalilansu na barin jam'iyar sun zargi shugaban nasu da taka dokokin jam'iyar,da kauce ma akidar jam'iyar, sannan kuma ya mayar da jam'iyar kamar kayan gado.