Ban Ki-Moon ya nemi duniya ta taimakawa Pakistan

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon ya bukaci duniya da ta kara bayar da goyon bayanta ga kasar Pakistan da ambaliyar ruwa ta yi wa kaca - kaca.

Ya ce gagarumar ambaliyar ruwan da ba a taba gani ba, na bukatar martanin da ba a taba gani ba.

Ya bayyana cewar Majalisar Dinkin Duniya za ta bayar da karin dala miliyan goma daga asusunta na bayar da agajin gaggawa.

Majalisar Dinkin Duniya ta nemi dala kusan miliyan dari biyar domin bukatun gaggawa na Pakistan.

Da yake magana a Pakistan bayan ganawa tare da Shugaban kasa da Firaminista, Mr Ban ya ce ba zai taba mantawa da wahalhalu da kuma barnar da ya gani ba.

Ya ce a baya na ziyarci wuraren bala'o'i da yawa a ko'ina cikin duniya, amma babu wanda ya kai wannan.