Tattalin arzikin Japan na ja da baya

Japan na fuskantar komabayan tattalin arziki
Image caption Alkaluma a japan na nuni da cewar daga watan Afrilu zuwa na Yuni, tattalin arzikin kasar ya karu ne da darajar kaso daya cikin dubu kacal.

Bunkasar tattalin arzikin Japan ya ragu kwarai a cikin watanni ukun da suka gabata, inda alkaluman da hukuma ta fitar ke nuna cewa daga watan Afrilu zuwa na Yuni, tattalin arzikin ya karu ne da darajar kaso daya cikin dubu kacal.

Masana tattalin arziki dai na ganin abin ma zai kara lalacewa nan da 'yan watanni masu zuwa yayinda hauhawar darajar kudin Japan din wato Yen za ta haddasa raguwar masu sayen kayayyakin da kasar ke fitarwa zuwa kasashen ketare, abinda zai baiwa China damar dara Japan a karfin tattalin arziki.

Sai dai Dr. Martin Schulz na cibiyar Fujitsu dake Japan ya ce kasar za ta fi ciniki idan har China ta zartata a karfin arziki.

Dr. Martin yace a daya bangaren kuma China ce kasuwar gobe tunda nan hankalin 'yan kasuwa ya karkata, don haka idan har habbakar tattalin arzikin China ya kere na Japan, alheri ne ga Japan din