Amai da gudawa ya kashe mutane 40 a Bauchi

Taswirar Nijeriya
Image caption kusan kowace shekara dai akan samu barkewar cutar amai da gudawa a wau jihohin Najeriya

Rahotanni daga Najeriya sun ce sama da mutum arba`in ne suka rasu sakamakon barkewar cutar amai da gudawa a jihar Bauchi da ke Arewa-maso-Gabashin kasar.

Mahukunta a jihar sun bayyana cewa cutar ta yi kamari ne a fadar jihar da kuma karamar hukumar Ganjuwa.

Sai dai a cewarsu yanzu sun shawo kan al`amarin. Rashin ingantaccen ruwan sha na daga cikin abubuwan da ke haddasa cutar amai da gudawa a lokuta da dama.

Har ila yau mahukunta a jihar Bauchi sun tabbatar da cewa sama da mutum dubu daya da dari biyu ne suka harbu da cutar amai da gudawa a jihar a cikin wata guda, musamman ma a karamar hukumar Ganjuwa da kuma fadar jihar.

Kuma kawo yanzu sama da mutum arba`in da bakwai ne suka rasu, yayin da ake ci gaba da jinyar wadanda ke harbuwa da cutar a sansanonin da aka kebe musu.

'Jama'a na ziyartar asibitoci domin samun magani'

Alhaji Mohammed Yahaya Jalam shi ne kwamishinan lafiya na jihar Bauchi. Kuma ya yiwa wakilin BBC Ibrahim Isa karin bayani ta wayar tarho a kan al`amarin.

Kwamishinan ya ce lamarin ya faru ne a yankuna daban daban na jihar, kuma har yanzu jama'a na ziyartar asibitoci domin samun magani.

A cewar Dakta Musa Mohammed Dambam wanda shi ne shugaban Hukumar kula da lafiya matakin farko na jihar Bauchi, cunkuso da rashin tsafta shi ne ummul'aba'isin abinda ya haifar da wannan matsala.

Sannan ya ce sune ci gaba da wayar da kan jama'a domin kaucewa ci gaba da yaduwar lamarin.

A kusan kowace shekara dai akan samu barkewar cutar amai da gudawa a wasu jihohin arewacin kasar. Ko da a baya-bayan nan cutar ta barke a jihar Adamawa da Gombe da Borno har ta yi sanadin rasuwar mutane da dama.

Ci gaba da barkewar annobar dai za iya cewa wata manuniya ce dangane da kalubalen da ke gaban mahukunta na su tashi haikan wajen wadata al`umarsu da ingantaccen ruwan sha.