Al'ummar Igbo sun ce zasu marawa Goodluck baya

Goodluck Jonathan
Image caption Goodluck Jonathan

A Nijeriya shugabannin al'ummar kabilar Igbo da ke sashen kudu maso gabashin kasar sun bayyana cewar zasu marawa Shugaba Goodluck Jonathan baya a takarar shugabancin kasar.

Shugabannin al'ummar Igbon sun bayyana haka ne bayani wani taro da suka yi a birnin Enugu.

Taron wanda ya hada sarakunan gargajiya da manyan 'yan kasuwa da kuma 'yan siyasar yankin kudu maso gabashin Nijeriya, an gudanar da shi ne a daidai lokacin da bangarori daban daban na Nijeriyar ke gudanar da taruka suna bayyana matsayinsu game da tsarin karba karba kan shugabanci, tsakanin sassa daban daban na kasar.

A kwanakin baya ne, gwamnonin jihohin kudu maso kudancin Nigeria suka bayyana matsayinsu inda suka ce zasu marawa Dr Goodluck Jonathan baya idan har ya fito takarar shugabanci a zaben da za'a yi badi.

Shi dai Dr Goodluck Jonathan bai bayyana cewar zai tsaya takara a zaben shugaban kasar da zaa yi ba a badi.