Ana ci gaba da kara samun bayani kan hadarin da aka yi a hanyar Legas zuwa Badun

A Nijeriya, ana ci gaba da samun karin bayani game da wani mummunan hadarin motoci da ya faru a jiya, a kan hanyar Lagos zuwa Badun.

Ana dai cewar hadarin yayi sanadiyar mutuwar mutane kusan arba'in,wasu mutanen masu yawa kuma sun samu raunuka.

Hadarin da ya kuma hada da motoci kimanin ashirin.

Shedu sun ce lamarin ya faru ne a wani wurin duba ababen hawa na yansanda.

Har yanzu dai hukumomin yansandan ba su bayar da bayani kan musabbin hadarin ba.