Karancin abinci na kara kamari a Nijar

karancin abinci a Nijar
Image caption Mata da kananan yara na daga cikin wadanda matsalar ta fi shafa

Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce matsalar abincin da ake fama da ita a Nijar ta haura ta shekara ta 2005, bayanda akalla rabin jama'ar kasar ke cikin matsananciyar bukatar taimakon abinci.

Mai magana da yawun hukumar ya ce mazauna yankunan karkara a Nijar, sun misalta halin da ake ciki da cewa ya fi na shekara ta 2005 muni, lokacin da dubban jama'a suka mutu saboda yunwa.

Bayan da aka shafe tsawon lokaci ana fama da mummunan fari, a yanzu an samu ruwa sosai a wasu sassa na kasar, inda akalla mutane shida suka rasa rayukansu.

Hukumar abincin tace kashi 17 cikin dari ko kuma daya cikin yara biyar a kasar, ba sa samun abinci mai gina jiki.

Alkaluman binciken da aka gudanar a watan Mayu da Juni - sun haura adadin da hukumar ta shata domin saka dokar tabaci.

Tana dai neman taimakon dala miliyan 213, sai dai har yanzu ana bukatar kashi 40 cikin dari na kudin, a cewar mai magana da yawun hukumar.

Image caption Noma da kiwo su ne mahimman abubuwan da jama'ar Nijar suka dogara da su

'Matsalar yunwa'

Kungiyar bada agaji ta Helen Keller International (HKI), ta soki kasashen duniya da gazawa wajen tunkarar matsalar da Nijar din ke fama da ita.

Babban daraktan kungiyar mai kula da nahiyar Afrika, Shawn Baker, ya shaidawa BBC cewa dubban yara ne za su rasa rayukansu muddum ba a samar da karin taimako ba.

"Yunwa kalma ce mai nauyi, amma idan ka kalli adadin yaran da abin ya ritsa dasu, da yadda amfanin gona ya mutu da kuma yadda jama'a suka rinka yin kaura a farkon bana, za ka iya fahimtar akwai matsalar yunwa."

Ya kara da cewa gwamnatin kasar ta Nijar tana yin iya yinta.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutane 67,000 ne suka rasa gidajensu, sakamakon wata ambaliyar ruwa a makon da ya wuce.

Image caption Nijar ta yi fama da matsalar yunwa a shekara ta 2005

Kogin River Niger - wanda shi ne mafi girma na uku a Afrika - ya yi cika mafi girma a shekaru 80, kamar yadda mahukunta suka bayyana.

Sai dai ruwan ya zo a makare, domin tuni amfanin gona ya riga ya lalace.

"Bana bala'in ya yi yawa," kamar yadda Christy Collins ta kungiyar agaji ta Mercy Corps ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AP.

Ta kara da cewa a yawancin shekaru, koda amfanin gona na farko ya lalace, akalla na baya-baya kan tsira.

A bana ba a samu ruwa mai yawa lokacin shuka ba, abinda yasa ciyawar da dabbobi ke ci ta mutu.

Ba wai kawai mazauna yankunan karkara na fama da karancin abinci bane, amfanin gonarsu - wanda shi ne kadai abinda suka dogara akai - sun lalace.