Majalisar dinkin duniya ta ce duuban yara ne za su kamu ta cututtuka a Pakistan

Majalisar dinkin duniya tayi gargadin cewa rayuwar yara kimanin miliyan uku da dubu dari biyar na cikin hadari daga cututtuka masu yaduwa ta hanyar ruwa bayan masifar ambaliyar ruwa da ta abka ma kasar.

Kira neman tallafi daga majalisar dinkin duniya na zo ne daidai lokacin da masifar ke dada muni inda ruwa ya mamaye sabbin yankuna a kudancin Pakistan.

Majalisar dinkin duniya ta kaddamar da gidauniyar neman dala miliyan dari hudu da sittin, to amma kawo yanzulilan ne daga cikin wannan adadi ya samu.

Wadanda suka tsira da rayukansa sun fusata da tafiyar hawainiyar da ake yi wajen agaza masu.