Ambaliyar ruwa a Pakistan na barazana ga yara sama da miliyan 3

Kananan Yara na tagayyara a Pakistan
Image caption Kananan Yara na tagayyara a Pakistan

Majalisar Dinkin Duniya tayi gargadin cewa yara kanana kusan miliyan 3 da rabi ne a kasar Pakistan suke fuskantar barazanar kamuwa da cuttukan dake yaduwa ta ruwa, a yayinda bala'in ambaliyar ruwa ke ci gaba da haifar da matsala.

Majalisar Dinkin Duniyar ta ce akwai bukatar samar da tallafi cikin gaggawa domin samar da tsabtataccen ruwan sha ga yaran da suka kai kimanin million 6.

Hukumomin Pakistan sun ce sun tashi tsaye haikan wajen neman agaji.

Ambaliyar ruwan dai ta mamaye kashi daya cikin biyar na fadin kasar baki daya.

Ministan harkokin wajen Pakistan Shah Mahmoud Qureshi ya ce kasarsa na cikin wani mawuyacin lokaci. Mr Qureshi ya ce akwai yuwuwar miliyoyin jama'a su kamu da yunwa, haka nan kuma masu tsattsauran ra'ayi su yi amfani da wannan dama wajen jan ra'ayin wasu da suka tsira.