Nijar ta shirya murkushe barazanar ta'addanci

Shugaban mulkin sojan Nijar Janar Salou Djibo
Image caption Shugaban mulkin sojan Nijar Janar Salou Djibo

Hukumomin Nijar sun ce turawan da ke bada agaji a wasu sassan kasar ba su da hujjar janyewa daga yankunan da suke aiki.

Gwamnatin Nijar din ta bakin kakakin ta, Dokta Mahamane Laouali Danda, ta ce tana cikin shirin ko-ta kwana, na murkushe duk wata barazanar ta'addanci.

A kwanakin baya ne wasu kungiyoyin agaji suka bada sanarwar janye ma'aikatansu Turawa daga wasu jihohi da suka hada da Tahoua da Maradi da Zinder, a kan barazanar kai masu hare hare daga wasu kungiyoyi masu daukar makamai.

Gwamnatin Nijar din ta kuma yi kira ga 'yan kasar da su koyi dogaro da kai wajen magance matsalolin da suka dame su.