An ba shugaban Najeriya wa'adi kan dokokin zabe

Majalisar dokokin Najeriya
Image caption Majalisar dokokin Najeriya

Bangaren marasa rinjaye na majalisar wakilan Najeriya ya koka da bangaren zartarwa, sakamakon jinkirin da shugaban kasar ke yi wajen rattaba hannu a kan dokokin zabe da kuma kasafin kudin kasar, wadanda majalisun dokokin suka zartar a kwanan nan.

Marasa rinjayen, ta bakin shugabansu Honourable Mohammed Ali Ndume, sun ce basu ga dalilin da ya sa shugaba Goodluck Jonathan ke jan-kafa wajen sa-hannu a kan dokokin ba, kasancewar ana matukar bukatar hakan.

'Yan majalisar dai sun yi barazanar za su nemi majalisar wakilan ta tabbatar da dokokin, idan har suka cika kwanaki talatin da zartarwa, shugaban kasar bai sa hannu a kansu ba.