Sabbin alkawurran agazawa kasar Pakistan

Mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Pakistan
Image caption Mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Pakistan

Mahukunta a Pakistan sun bayyana cewa, an yi masu sabbin alkawuran agajin da ya zarta dala miliyan 300, domin fuskantar bala'in ambaliyar ruwan da ta lalata kusan rabin kasar.

An yi sabbin alkawuran ne, bayanda kwamitin kai agajin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya ya ce, kudaden da ya samu basu wuce kimanin kashi daya bisa 3 na abinda yake bukata ba.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce har yanzu miliyoyin mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa a Pakistan din, basu sami wani taimako ba.

Jakadan Pakistan a ofishin Majalisar dake Geneva, Zamir Akram, ya ce wani yankin kasar da girmansa zai kai Ingila, yanzu haka ruwa ya mamaye shi, kuma za a kwashe shekaru kafin a iya sake gina shi.