Kamfanin BP ya musanta kawar da kai a malalar man tekun Mexico

Rijiyar man BP
Image caption Rijiyar man BP

Kampanin mai na BP ya yi watsi da zargin cewa a karo da dama ya sha kawar da kai wajen ba da bayanai kan bindigar da wata rijiyar mai ta yi a tekun Mexico, lamarin da ya haddasa malalar mai mafi muni a tarihin Amurka.

Zargin na kunshe ne cikin wata wasika da Transocean din ya rubuta wadda ke cewa.

BP na ci gaba da nuna jan kafa, ko yin kememe wajen bada bayanai, duk kuwa saukinsu in ji kampanin Transocean.

Sai dai wani mai magana da yawun kampanin na BP ya ce zargin ba gaskiya ba ne, kuma yaudara ce.

Ya ce an yi zargin ne da nufin nuna cewar kampanin na Transocean ba shi da wani laifi a aukuwar hadarin.