Kamfanin matambayi baya bata na Google yayi gargadi

Shugaban babban kamfanin matambayi ba ya bata na Google, yayi babban kashedi dangane da yawan bayanan da jama'a ke bari a shafufukan intanet.

Eric Schmidt ya ce dole a nan gaba wasu matasa su sauya irin bayyanan da suka shafe su, saboda kurar da suka bari a shafufukan na intanet.

Da ma dai a lokutan baya an soki kamfanin na Google, kan yadda ya ke sarrafa irin bayyanan da suka shafi jama'a.