An kashe sojojin India 3 a kasar Congo

Sojojin Kiyaye zaman lafiya
Image caption Sojojin Kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Congo

'Yan tawaye sun kashe sojojin kasar India 3, wadanada ke aikin samar da zaman lafiya a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

Rundunar sojin India ta ce an kai harin ne a tsakiyar dare kan sansanin sojin da ke da nisan kilo mita 14 a Arewacin garin Goma.

An dora alhakin harin kan 'yan tawayen yankin da aka fi sani da Mai Mai.

Jami'an soji suka ce wasu mutane biyar ne suka nufi sansanin sojin a tsakiyar dare, amma a lokacin da suke tattaunawa da masu gadi, sai wasu 'yan tawaye kimanin 50 suka bude wuta kan sansanin.

'Yan tawayen sun yi amfani da wuka da adduna, inda suka kashe uku daga cikin sojojin, sannan suka raunata bakwai.

Kimanin sojoji 20,000 ke aikin samar da zaman lafiya a kasar ta Congo - kuma shi ne aikin samar da zaman lafiya mafi girma a duniya.